Menu

Zabura 110

BIB

1 Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna a hannun damana, sai na sa abokan gābanka su zama matashin sawunka.”

2 Ubangiji zai fadada ikon sandan mulkinka daga Sihiyona za ka yi mulki a tsakiyar abokan gābanka.

3 Rundunarka za su so yin yaƙi a ranarka ta yaƙi. Saye cikin ɗaukaka mai tsarki, daga cikin ciki na safiya za ka karɓi raɓar ƙuruciyarka.

4 Ubangiji ya rantse ba zai kuma canja zuciyarsa ba, “Kai firist ne har abada, bisa ga tsarin Melkizedek.”

5 Ubangiji yana a hannun damanka; zai murƙushe sarakuna a ranar fushinsa.

6 Zai hukunta al’ummai, yana tarawa gawawwaki yana kuma murƙushe masu mulkin dukan duniya.

7 Zai sha daga rafin da yake kusa da hanya; saboda haka zai ɗaga kansa sama.

Everything we make is available for free because of a generous community of supporters.

Donate