Menu

Zabura 120

BIB

1 Na yi kira ga Ubangiji cikin damuwata, ya kuwa amsa mini.

2 Ka cece ni, ya Ubangiji, daga leɓuna masu ƙarya da kuma daga harsuna masu yaudara.

3 Me zai yi maka, me kuma ya fi, ya kai harshe mai yaudara?

4 Zai hukunta ku da kibiyoyi masu tsini na jarumi, tare da garwashin wuta na itacen tsintsiya.

5 Kaitona da nake zama a Meshek, da nake zama a ciki tentunan Kedar!

6 Da daɗewa na zauna a cikin waɗanda suke ƙin salama.

7 Ni mutum ne mai salama; amma sa’ad da na yi magana, su sai su yi ta yaƙi.

Everything we make is available for free because of a generous community of supporters.

Donate