Menu

Zabura 16

BIB

1 Ka kiyaye ni, ya Allah, gama a cikinka nake samun mafaka.

2 Na ce wa Ubangiji, “Kai ne shugabana; in ba tare da kai ba, ba ni da wani abu mai kyau.”

3 Game da tsarkakan da suke cikin ƙasar kuwa, su ne masu ɗaukakar da dukan farin cikina ya dangana.

4 Baƙin ciki zai ƙaru wa waɗanda suke bin waɗansu alloli. Ba zan zuba musu hadayarsu ta jini ba ko in ambaci sunayensu da bakina.

5 Ubangiji, ka ba ni rabona da kwaf ɗin na; ka kiyaye rabona,

6 Iyakoki sun fāɗo mini a wurare masu daɗi; tabbatacce ina da gādo mai bansha’awa.

7 Zan yabi Ubangiji, wanda yake ba ni shawara; ko da dare ma zuciyata kan koya mini.

8 Kullum nakan sa Ubangiji a gabana. Gama yana a hannun damana, ba zan jijjigu ba.

9 Saboda haka zuciyata tana murna harshena kuma yana farin ciki; jikina kuma zai zauna lafiya,

10 domin ba za ka yashe ni a kabari ba, ba kuwa za ka bar Mai Tsarkinka yă ruɓa ba.

11 Ka sanar da ni hanyar rai; za ka cika ni da farin ciki a gabanka, da madawwamin jin daɗi a hannun damarka.

Everything we make is available for free because of a generous community of supporters.

Donate