Menu

Zabura 29

BIB

1 Ku ba da girma ga Ubangiji, ya ku manya, ku ba da girma ga Ubangiji saboda ɗaukaka da kuma ƙarfinsa.

2 Ku ba da girma ga Ubangiji, ɗaukakar da ta dace da sunansa; ku bauta wa Ubangiji cikin ɗaukakar tsarkinsa.

3 Muryar Ubangiji tana a bisa ruwaye; Allah Maɗaukaki ya yi tsawa, Ubangiji ya yi tsawa a bisa manyan ruwaye.

4 Muryar Ubangiji mai iko ce; muryar Ubangiji da girma take.

5 Muryar Ubangiji ta kakkarya itatuwan al’ul na Lebanon. Ubangiji ya kakkarya itatuwan al’ul na Lebanon kucu-kucu.

6 Ya sa dutsen Lebanon ya yi ta tsalle kamar ɗan maraƙi, Siriyon kuma kamar ɗan jakin jeji.

7 Muryar Ubangiji ta buga da walƙatar walƙiya.

8 Muryar Ubangiji ta girgiza hamada Ubangiji ya girgiza Hamadan Kadesh.

9 Muryar Ubangiji ta murɗa itatuwan oak ya kakkaɓe itatuwan kurmi. Kuma a cikin haikalinsa kowa ya ce, “Ɗaukaka!”

10 Ubangiji na zaune yana sarauta a bisa rigyawa; Ubangiji yana sarauta kamar Sarki har abada.

11 Ubangiji kan ba da ƙarfi ga mutanensa; Ubangiji kan albarkace mutanensa da salama.

Everything we make is available for free because of a generous community of supporters.

Donate