Menu

Zabura 54

BIB

1 Ka cece ni, ya Allah ta wurin sunanka; ka nuna ni marar laifi ne ta wurin ƙarfinka.

2 Ka ji addu’ata, ya Allah; ka saurari maganar bakina.

3 Baƙi suna kawo mini hari; mutane marasa imani suna neman raina, mutanen da ba sa tsoron Allah. Sela

4 Tabbatacce Allah ne mai taimakona, Ubangiji shi ne wanda yake riƙe ni.

5 Bari mugunta ta shaƙe masu magana marar kyau a kaina; cikin amincinka ka hallaka su.

6 Zan miƙa hadaya ta yardar rai gare ka; zan yabe sunanka, ya Ubangiji, gama yana da kyau.

7 Gama ya cece ni daga dukan wahalolina, idanuna kuma sun ga an yi nasara a kan maƙiyana.

Everything we make is available for free because of a generous community of supporters.

Donate