Menu

Zabura 70

BIB

1 Ka hanzarta, ya Allah, ka cece ni; Ya Ubangiji, zo da sauri ka taimake ni.

2 Bari masu neman raina su sha kunya su kuma rikice; bari dukan masu sha’awar gani lalacewata su juye baya da kunya.

3 Bari masu ce mini, “Allah yă ƙara!” Su juye baya saboda kunyansu.

4 Amma bari dukan masu nemanka su yi farin ciki su kuma yi murna a cikinka; bari waɗanda suke ƙaunar cetonka kullum su ce, “Bari Allah yă sami ɗaukaka!”

5 Duk da haka ni matalauci ne da kuma mai bukata; ka zo da sauri gare ni, ya Allah. Kai ne mai taimakona da mai cetona; Ya Ubangiji, kada ka yi jinkiri.

Everything we make is available for free because of a generous community of supporters.

Donate