Menu

Zabura 98

BIB

1 Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji, gama ya yi abubuwa masu banmamaki; hannunsa na dama da hannunsa mai tsarki sun yi masa aikin ceto.

2 Ubangiji ya sanar da cetonsa ya kuma bayyana adalcinsa ga al’ummai.

3 Ya tuna da ƙaunarsa da kuma amincinsa ga gidan Isra’ila; dukan iyakar duniya sun ga ceton Allahnmu.

4 Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, dukan duniya, ku ɓarke da waƙa ta murna tare da kiɗi;

5 ku yi kiɗi ga Ubangiji da garaya, da garaya da ƙarar rerawa,

6 tare da bushe-bushe da karar ƙahon rago, ku yi sowa don farin ciki a gaban Ubangiji, Sarki.

7 Bari teku su yi ruri, da kuma kome da yake cikinsa, duniya da kuma kome da yake cikinta.

8 Bari koguna su tafa hannuwansu, bari duwatsu su rera tare don farin ciki;

9 bari su rera a gaban Ubangiji, gama yana zuwa domin yă hukunta duniya. Zai hukunta duniya da adalci mutane kuma cikin gaskiya.

Everything we make is available for free because of a generous community of supporters.

Donate