Menu

Zabura 100

BIB

1 Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, dukan duniya.

2 Yi wa Ubangiji sujada da murna; ku zo gabansa da waƙoƙin farin ciki.

3 Ku san cewa Ubangiji shi ne Allah. Shi ne ya yi mu, mu kuwa nasa ne; mu mutanensa ne, tumakin makiyayarsa.

4 Ku shiga ƙofofinsa da godiya filayen gidansa kuma da yabo; ku gode masa ku kuma yabi sunansa.

5 Gama Ubangiji yana da kyau kuma ƙaunarsa madawwamiya ce har abada; amincinsa na cin gaba a dukan zamanai.

Everything we make is available for free because of a generous community of supporters.

Donate