Menu

Zabura 101

BIB

1 Zan rera wa ƙauna da adalcinka; gare ka, ya Ubangiji, zan rera yabo.

2 Zan yi hankali ga yin rayuwa marar zargi, yaushe za ka zo gare ni? Zan bi da sha’anin gidana da zuciya marar abin zargi

3 Ba zan kafa a gaban idanuna 1 wani abu marar kyau ba. Na ƙi jinin ayyukan mutane marasa aminci; ba za su manne mini ba.

4 Mutane masu mugun zuciya za su nesa da ni; ba abin da zai haɗa ni da mugunta.

5 Duk wanda ya yi ɓatanci wa maƙwabcinsa a ɓoye shi za a kashe; duk mai renin wayo da mai girman kai, ba zan jure masa ba.

6 Idanuna za su kasance a kan amintattu a cikin ƙasar, don su zauna tare da ni; tafiyarsa ba ta da zargi zai yi mini hidima.

7 Babu mai ruɗun da zai zauna a gidana; babu mai ƙaryan da zai tsaya a gabana.

8 Kowace safiya zan rufe bakunan dukan mugaye a ƙasar; zan yanke kowane mai aikata mugunta daga birnin Ubangiji.

Everything we make is available for free because of a generous community of supporters.

Donate