Menu

Zabura 128

BIB

1 Masu albarka ne dukan masu tsoron Ubangiji, waɗanda suke tafiya a hanyoyinsa.

2 Za ka ci amfanin aikinka; albarku da wadata za su zama naka.

3 Matarka za tă zama kamar kuringar inabi mai ’ya’ya a cikin gidanka; ’ya’yanka maza za su zama kamar tohon zaitun kewaye da teburinka.

4 Ta haka mai albarka yake wanda yake tsoron Ubangiji.

5 Bari Ubangiji ya albarkace ka daga Sihiyona dukan kwanakin ranka; bari ka ga wadatar Urushalima,

6 bari kuma ka rayu ka ga ’ya’ya ’ya’yanka. Salama tă kasance tare da Isra’ila.

Everything we make is available for free because of a generous community of supporters.

Donate