Menu

Zabura 63

BIB

1 Ya Allah, kai ne Allahna, da nacewa na neme ka; raina yana ƙishinka, jikina yana marmarinka, cikin busasshiyar ƙasar da ta zozaye inda babu ruwa.

2 Na gan ka a wuri mai tsarki na kuma dubi ikonka da ɗaukakarka.

3 Domin ƙaunarka ta fi rai kyau, leɓunana za su ɗaukaka ka.

4 Zan yabe ka muddin raina, kuma a cikin sunanka zai ɗaga hannuwana.

5 Raina zai ƙoshi kamar da abinci mafi kyau; da leɓunan rerawa bakina zai yabe ka.

6 A gadona na tuna da kai; ina tunaninka dukan dare.

7 Domin kai ne mai taimakona, ina rera a cikin inuwar fikafikanka.

8 Raina ya manne maka; hannunka na dama yana riƙe da ni.

9 Su da suke neman raina za su hallaka; za su gangara zuwa zurfafan duniya.

10 Za a bayar da su ga takobi su kuma zama abincin karnukan jeji.

11 Amma sarki zai yi farin ciki ga Allah; dukan waɗanda suke rantse da sunan Allah za su yabe shi, amma za a rufe bakunan maƙaryata.

Everything we make is available for free because of a generous community of supporters.

Donate