Menu

Zabura 64

BIB

1 Ka ji ni, ya Allah, yayinda nake faɗin abin da yake damuna; ka tsare raina daga barazanan abokin gāba.

2 Ka ɓoye ni daga ƙulle-ƙullen mugaye, daga daure dauren wannan taro masu aikata mugunta.

3 Sukan wāsa harsunansu kamar takuba su harba kalmominsu kamar kibiyoyi masu kisa.

4 Sukan yin kwanto su harbi marar laifi; sukan yi harbi nan da nan, ba tsoro.

5 Sukan ƙarfafa juna a mugayen ƙulle-ƙullensu, sukan yi magana yadda za su ɓoye tarkunansu; su ce, “Wa zai gan su?”

6 Sukan yi ƙulle-ƙullen rashin adalci su ce, “Mun gama ƙulla cikakkiyar maƙarƙashiya tsab!” Zuciyar mutum da tunaninsa, suna da wuyar ganewa.

7 Amma Allah zai harbe su da kibiyoyi; nan da nan za a buge su su fāɗi.

8 Zai juya harshensu a kansu yă kuma kawo su ga hallaka; duk waɗanda suka gan su za su kaɗa kai, suna musu ba’a.

9 Dukan mutane za su ji tsoro; za su yi shelar ayyukan Allah su kuma yi tunanin abin da ya aikata.

10 Bari masu adalci su yi farin ciki a cikin Ubangiji su kuma nemi mafaka a gare shi; bari dukan masu gaskiya a zuciya su yabe shi!

Everything we make is available for free because of a generous community of supporters.

Donate